Lahadi 20 Satumba 2026 - 18:38
Bayanin Shahidin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Kan Ɗaukaka da Girman Imam Hasan Askari (A.S)

Hauza/ Rayuwar Imam Hasan Askari (A.S) ta kasance cikin tsananin matsin lamba da zaman baƙunci. Duk da haka, a zamaninsa da kuma zamanin Imamai da suka gabace shi, hulɗa da alaƙar mabiya mazhabar Jafariyya sun ƙaru sosai. Bayanan Shahidin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, sun sake bayyana irin wannan gwagwarmaya, tasirin zamantakewa da kuma faɗin alaƙar Imam Hasan Askari (A.S) da al’umma.

A yayin tunawa da zagayowar ranar haihuwar Imam Hasan Askari (A.S), Kamfanin Dillancin Labaran Hauza na gabatar muku, ya ku masu karatu, da wani ɓangare na bayanan Imam Shahidin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, dangane da halayen wannan babban Imam.

1. Masu adawa sun amince da falala, jarumtaka da juriyar Imam Hasan Askari (A.S)

Wannan Imam ne wanda masoyansa, mabiya Shi’a, masu adawa da shi da kuma waɗanda ba su yi imani da shi ba, duk suka shaida kuma suka amince da falalarsa, iliminsa, taƙawarsa, tsarkinsa, ismarsa, jarumtarsa a gaban maƙiyansa, da kuma haƙurinsa da juriyarsa a lokacin wahalhalu.

Wannan babban mutum mai ɗaukaka ya yi shahida yana da shekaru ashirin da takwas kacal.

A cikin tarihin Shi’a mai cike da alfahari, muna da irin waɗannan misalai da yawa. Mahaifin Imam Mahdi (A.F), duk da yawan falaloli, matsayi da mu’ujizozin da yake da su, lokacin da ya rasu sakamakon guba ta hannun maƙiyansa, yana da shekaru ashirin da takwas kacal. Wannan shi ne abin koyi. Matashi yana jin cewa yana da babban misali a gabansa.

Imam Muhammad Jawad (A.S), wanda shi ne baban Imam, an shahadantar da shi yana da shekaru ashirin da biyar. Haka kuma Imam Hasan Askari (A.S) ya yi shahada yana da shekaru ashirin da takwas.

Duk da yawan falaloli, karamomi da ɗaukakar da waɗannan Imamai suke da ita, ba mu kaɗai ne muka amince da su ba ko kuma muke yabonsu. Har ma maƙiyansu da masu adawa da su, waɗanda ba su yi imani da imamancinsu ba, duk sun amince da irin wannan ɗaukaka.

Madogara: Jawabin ganawa da wasu daga cikin al’umma, iyalan shahidai da waɗanda suka sadaukar da kansu — 10/12/1390 (2 ga Maris, 2012).

2. Da’awar imamanci ce ta sa mahukunta suka ƙi jinin Ahlul Baiti (A.S)

Waɗannan manyan mutane, wato Imamai (A.S), a kodayaushe suna cikin gwagwarmaya. Gwagwarmayar tasu tana da alaƙa da harkokin siyasa, domin wanda yake zaune a kan kujerar mulki shi ma yana da’awar bin addini.

Shi ma yana kula da zahirin addini, kuma a wasu lokuta har yana amincewa da ra’ayin addini na Imam. Kamar yadda kuka ji game da wasu abubuwan da suka faru a zamanin Ma’amun, inda ya amince kai tsaye da ra’ayin Imam.

Wato ba sa ƙin amincewa da ra’ayin fikihu na Imam a wasu lokuta. Abin da ya sa aka samu wannan gwagwarmaya da adawa tsakanin mahukunta da Ahlul Baiti shi ne, Ahlul Baiti suna ɗaukar kansu a matsayin Imamai. Suna cewa: “Mu ne Imamai.”

Imam Baƙir (A.S), a wani taro da ya halarta a Mina, ya ce:

«إِنَّ رَسُولَ اللهِ كَانَ الْإِمَامَ»

“Lallai Manzon Allah ya kasance shi ne Imam.”

Sai ya ambaci Imamai ɗaya bayan ɗaya har ya zo kansa, ya ce: “Ni ma Imam ne.”

Wannan shi ne babban ginshiƙin gwagwarmayar da suke yi da mahukunta. Domin wanda ya hau mulki kuma yake ɗaukar kansa a matsayin Imam kuma jagora, yana ganin cewa alamomi da sharuɗɗan da ya kamata su kasance a tare da Imam suna tattare da wannan mutum (Imam), amma ba su tare da shi kansa.

Saboda haka, yana kallon Imam a matsayin barazana ga mulkinsa, domin Imam yana da’awar jagoranci.

Mahukunta suna yaƙi da wannan ruhin gwagwarmaya, yayin da Imamai (A.S) suke tsayawa da ƙarfi kamar dutse.

A bayyane yake cewa a cikin wannan gwagwarmaya, koyar da ma’arifar addini, hukunce-hukuncen fikihu, akhlak da kyawawan halaye da Imamai suke yaɗawa, duk suna da matsayinsu.

Yawan ɗaliban da suke horarwa da kuma faɗaɗar alaƙar mabiya Shi’a suna ƙaruwa kowace rana. Wannan ne ya kiyaye Shi’a.

Ku yi la’akari da wata akida da aka yi mulki a kanta tsawon shekaru 250! A zahiri, ya kamata babu abin da ya rage daga cikinta; ya kamata ta ɓace gaba ɗaya. Amma ku duba yadda duniya take a yau, da kuma matsayin da Shi’a ta kai!

Ya kamata a fahimci wannan batu sosai a cikin waƙoƙin da ake karantawa game da Imam Sadiƙ, Imam Hadi da Imam Hasan Askari (A.S).

Waɗannan Imamai sun yi gwagwarmaya, kuma saboda wannan gwagwarmaya ne suka rasa rayukansu. Hanya ce da take ci gaba zuwa ga wata manufa bayyananniya. Wani lokaci mutum yana juyawa, wani kuma yana bin wata hanya, amma manufar ɗaya ce. (Madogara: 30/06/1380 (21 ga Satumba, 2001)).

3. Alaƙar mabiya Shi’a a zamanin Imam Jawad zuwa Imam Askari ta fi kowanne lokaci yaɗuwa

A zamanin Imam Rida, Imam Jawad, Imam Hadi da Imam Hasan Askari (A.S), alaƙar mabiya Shi’a ta fi kowanne lokaci yaɗuwa.

Ba a taɓa samun alaƙar mabiya Shi’a da faɗaɗar tsarinsu a sassa daban-daban na duniyar Musulunci kamar yadda aka samu a zamanin Imam Jawad, Imam Hadi da Imam Hasan Askari ba.

Kasancewar wakilai da mataimaka, da kuma labaran da ake bayarwa game da Imam Hadi da Imam Hasan Askari — kamar labarin mutumin da ya kawo kuɗi, sai Imam ya bayyana masa abin da ya kamata a yi da kuɗin — duk suna nuna irin wannan faɗaɗar alaƙa.

Wannan na nufin cewa duk da kasancewar waɗannan manyan Imamai biyu a ƙarƙashin kulawa da takurawar mahukunta a Samarra, da kuma Imam Jawad da Imam Rida kafin su, alaƙarsu da mutane ta ci gaba da faɗaɗa.

Irin wannan alaƙa ta wanzu tun kafin zamanin Imam Rida. Sai dai zuwan Imam Rida zuwa Khurasan ya yi tasiri sosai wajen ƙarfafa ta. (Madogara: 18/05/1384 (9 ga Agusta, 2005)).

Ƙaruwar zaman baƙuncin Imamai uku

Gaskiya ne cewa waɗannan manyan Imamai sun rayu cikin tsananin baƙunci. Sun kasance nesa da Madina, nesa da iyalansu da kuma wuraren da suka saba rayuwa.

Amma akwai wani abu da ya kamata a kula da shi game da waɗannan Imamai uku, daga Imam Jawad zuwa Imam Hasan Askari. Shi ne cewa yayin da muke matsowa kusa da ƙarshen rayuwar Imam Hasan Askari, zaman baƙuncin da suka fuskanta yana ƙara tsananta.

Tasirin Imamai da faɗin da'irar mabiya Shi’a a zamanin waɗannan Imamai uku ya kai kusan ninki goma idan aka kwatanta da zamanin Imam Baƙir da Imam Sadiƙ.

Wannan abu ne mai ban mamaki. Wataƙila dalilin da ya sa aka tsananta musu da kuma takura musu shi ne wannan faɗaɗar tasiri da alaƙa. (Madogara: 20/02/1382 (10 ga Mayu, 2003)).

4. Imam Hasan Askari (A.S) ya kulla alaƙa da dukkan duniyar Musulunci daga birnin Samarra

Bayan Imam Rida (A.S) ya tafi Iran ya isa Khurasan, ɗaya daga cikin abubuwan da suka faru shi ne faɗaɗar alaƙar da aka samu tsakanin Imam da al'umma. Wataƙila wannan ma yana daga cikin abubuwan da Imam na takwas (A.S) ya yi la’akari da su.

Kafin wannan lokaci, mabiya Shi’a suna nan a wurare daban-daban, amma suna warwatse, ba su da alaƙa mai ƙarfi da juna, suna cikin rashin fata kuma ba su da wani kyakkyawan hangen nesa game da makomarsu. Mulkin halifofi kuma ya mamaye ko’ina. Kafin wannan ma, akwai mulkin Haruna mai tsananin ƙarfi da danniya.

Lokacin da Imam ya nufi Khurasan, ya bi wannan hanya, mutane suka ga wani babban mutum a gabansu, wanda ya nuna musu ilimi, ɗaukaka, girma, gaskiya da haske na ruhaniya.

Mutane ba su taɓa ganin mutum mai irin wannan hali ba. A baya, mutane nawa ne daga cikin mabiya Shi’a a Khurasan suke iya tafiya zuwa Madina domin ganawa da Imam Sadiƙ?

Amma a wannan doguwar hanya, mutane a wurare daban-daban sun samu damar ganin Imam da idonsu. Wannan abu ne mai ban mamaki; kamar mutum ya ga Manzon Allah ne.

Irin wannan girma da ɗaukaka ta ruhaniya, mutunci, kyawawan ɗabi’u, taƙawa, haske na ruhaniya da kuma faɗin iliminsa — inda duk abin da ka tambaye shi ko ka nema yake da shi — sun kasance abubuwan da mutane ba su taɓa gani ba.

Wannan ya haifar da gagarumin tasiri a tsakanin mutane.

Tasirin zuwan Imam Rida da shahadarsa

Imam ya isa Khurasan da Marw. Marw kuwa ita ce cibiyar yankin a wancan lokaci, kuma tana cikin ƙasar Turkmenistan ta yau.

Bayan shekara ɗaya ko biyu, Imam ya yi shahada, mutane suka shiga cikin baƙin ciki mai tsanani.

Zuwan Imam, wanda ya nuna wa mutane abubuwan da ba su taɓa gani ko ji ba, da kuma shahadarsa wadda ta jawo babban baƙin ciki, sun taimaka wajen samar da yanayi mai ƙarfi ga mabiya Shi’a a waɗannan yankuna.

Wannan ba yana nufin cewa dukkan mutane sun zama mabiya Shi’a ba ne, amma mutane da yawa sun zama masu ƙaunar Ahlul Baiti.

Faɗaɗar alaƙa a zamanin Imam Hadi da Imam Hasan Askari

Daga zamanin Imam Rida har zuwa shahadar Imam Hasan Askari (A.S), irin wannan gagarumin ci gaba ya faru.

Imam Hadi da Imam Hasan Askari, a birnin Samarra, wanda a zahiri yake kama da sansanin sojoji, sun sami damar tsara da kuma ƙarfafa alaƙa da dukkan sassan duniyar Musulunci.

Samarra ba babban birni ba ne irin wanda ake da shi a manyan wurare. Wata sabuwar cibiyar mulki ce da aka gina, wadda ake kira “Surra Man Ra’a”. A cikinta ne aka tattara manyan jami’an gwamnati, shugabanni da wasu mutanen gari da ake buƙata domin biyan bukatun yau da kullum.

Duk da haka, Imam Hadi da Imam Hasan Askari sun sami damar ƙulla waɗannan alaƙa masu faɗi.

Idan muka yi nazari kan ɓangarori daban-daban na rayuwar Imamai, za mu fahimci irin manyan ayyukan da suke gudanarwa.

Saboda haka, ba wai aikinsu ya tsaya ne kawai wajen amsa tambayoyi game da salla, azumi, tsarki da najasa ba. Sun kasance a matsayi na Imam, bisa ma’anar jagoranci ta Musulunci, kuma suna tattaunawa da mutane daga wannan matsayi.

A ganina, wannan ɓangare na rayuwarsu yana da matuƙar muhimmanci tare da sauran ɓangarorin rayuwarsu.

Ku duba yadda aka kawo Imam Hadi daga Madina zuwa Samarra, sannan aka shahadantar da shi yana da shekaru arba'in da biyu.

Haka kuma Imam Hasan Askari ya yi shahada yana da shekaru ashirin da takwas.

Waɗannan abubuwa duk suna nuna irin gagarumin motsi da Imamai (A.S), mabiya Shi’a da sahabbansu suka gudanar a tsawon tarihi.

Duk da cewa tsarin mulkin halifofi ya kasance mai tsananin sa ido da amfani da jami’an tsaro wajen danniya, Imamai (A.S) sun sami nasarar gudanar da ayyukansu ta wannan hanya. Abin da nake nufi shi ne, tare da ganin irin zaman baƙuncin da suka yi, ya kamata mu kuma fahimci irin mutunci, ɗaukaka da girman da suka samu. (Madogara: 20/02/1382 (10 ga Mayu, 2003)).

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha